Kafafen watsa labarun Amurka sun ambaci cewa, shugaban kasar Donald Trump ya bayar da umarnin dakatar da duk wani taimako na soja da ake bai wa Ukirnaiya, daga ciki har da makaman da ake kai wa ta sama da jiragen ruwa da kuma wadanda a halin yanzu sun isa kasar Poland.
Jaridar “Bloomberg” ta bayyana cewa; bayan kwanaki kadan da aka yi cacar baki a tsakanin shugaban na Amurka Donald Trump da kuma takwaransa na Ukiraniya Volodymyr Zelensky, shugaban na kasar Amurka ya bayar da umarnin a dakatar da bai wa Ukiraniya duk wani taimako na soja.
Wani jami’i a ma’aikatar tsaron Amurka ya bayyana cewa; “ Amurkan ta dakatar da duk wani taimako na soja da take bai wa Ukiraniya a halin yanzu, har zuwa lokacin da shugabannin kasar za su nuna cewa da gaske suna son zaman lafiya.”
Ita kuwa jaridar “Washington Post” ta nakalto cewa, jami’an gwamnatin Amurkan suna kuma nazarin yadda za su dakatar da musayar bayanai da suke yi da Ukiraniya, haka nan horon soja da ake ba su.”
A ranar juma’ar da ta gabata ne dai shugaban kasar Ukiraniya Volodymyr Zelensky ya kai ziyara Amurka, sai dai ba ta kare da dadi ba a tsakaninsa da shugaban kasar Donald Trump, saboda sabanin da su ka samu akan batun tsagaita wutar yaki da kuma yarjejeniya akan ma’adanai.
Trump ya zargi shugaban na Ukiraniya da kokarin kunna wutar yakin duniya na 3,alhali bai taki wani abu ba.