Trump ya ce zai yi shawara game da batun kafa kasar Falasdinu

Shugaban Amurka, Donald Trump ya ce zai yi shawara game da yiwuwar amincewa da kafa kasar Falasdinu a matsayin masalaha a yankin Gabas ta Tsakiya.

Shugaban Amurka, Donald Trump ya ce zai yi shawara game da yiwuwar amincewa da kafa kasar Falasdinu a matsayin masalaha a yankin Gabas ta Tsakiya.

Trump ya ce zai yi aiki tare da sauran kasashen duniya game da wannan batun.

Ya bayyana hakan ne ga ga manema labarai a kan hanyarsa ta komawa Amurka daga ziyarar da ya kai yankin Gabas ta Tsakiya ranar Litinin, domin sanya hannu kan yarjejeniyar tsagaita wuta a Gaza.

Ko a ranar Litinin ma yayin da yake tsaka da jawabi a majalisar dokokin Isra’ila, wani dan majalisa ya daga wata takarda dake bukatar Trump ya amince da kafuwar kasar Falasdinu.

To saidai  jami’an tsaron Isra’ilar sukayi waje da shi daga zauren.

Bukatar kafa kasar Falasdinu na ci gaba da wanzuwa a duniya musamman a kasashen yamma inda ko a baya-bayan nan kasashen duniya da dama sun yi ta kiraye-kiyaren amincewa da kafa kasar Falasdinu a babban taron MDD karo na 80.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments