Shugaban Amurka Donald Trump ya fada ya bayyana a wannan Laraba cewa ya yi tattaunawa mai kyau” da Volodymyr Zelensky, washegarin da ya tattauna ta wayar tarho da Vladimir Putin.
Ya kara da cewa tattaunawar ta yi armashi yayin da Amurka ke yunkurin tsagaita wuta a Ukraine.
“Na yi magana da shugaban Ukraine Zelensky, ta dauki kusan awa daya, kuma galibin tattaunawar ta ta’allaka ne kan kiran da suka yi da shugaba Putin na jiya domin daidaita batun kasashen Rasha da Ukraine, kuma “Muna kan hanya madaidaiciya,” inji shugaban na Amurka a shafinsa na True Social Network.
Tunda farko dama wakilin Amurka Steve Witkoff ya bayyana a ranar Talata bayan tattaunawa ta wayar tarho tsakanin shugaba Donald Trump da takwaransa na Rasha Vladimir Putin game da haduwar birnin Jeddah na kasar Saudiyya kan shirin tsagaita bude wuta a Ukraine.
Bayanai sun nuna cewa tawagar Amurkan da za ta je Saudiyya za ta kasance karkashin jagorancin sakataren harkokin wajen kasar Marco Rubio da kuma mai ba da shawara kan harkokin tsaro Mike Waltz, amma ba wai wadanda za su shiga tsakani ba.