Trump Ya Bukaci Gwamnatin Isra’ila Da Ta Daina Kai Hare-Hare Kan Zirin Gaza

Shugaban Amurka ya ce: Dole ne gwamnatin mamayar Isra’ila ta daina kai hare-hare kan Gaza nan take domin samun damar sakin fursunoninta Shugaban Amurka Donald

Shugaban Amurka ya ce: Dole ne gwamnatin mamayar Isra’ila ta daina kai hare-hare kan Gaza nan take domin samun damar sakin fursunoninta

Shugaban Amurka Donald Donald Trump, bayan da kungiyar Hamas ta fitar da martanin kan yarjejeniyar zaman lafiya a Gaza, ya yi kira ga gwamnatin mamayar Isra’ila da ta gaggauta dakatar da kai hare-hare a zirin Gaza.

Shugaban Amurka Donald Trump ya yi kira ga gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila a daren Juma’a da ta dakatar da harin bam da take kaiwa Gaza, yana mai cewa; “Dole ne gwamnatin mamayar Isra’ila ta gaggauta dakatar da kai hare-hare a zirin Gaza domin a samu damar zakulo mutanen da aka yi garkuwa da su cikin aminci da gaggawa.”

Da yake mayar da martani ga sanarwar da kungiyar Hamas ta fitar, Trump ya bayyana a wani sakon da ya wallafa a shafin Truth Social cewa: “Ya yi imani Hamas a shirye take ta samar da zaman lafiya mai dorewa.”

Shugaban na Amurka ya lura da cewa “Mun riga mun fara tattaunawa game da cikakkun bayanai da ya kamata a warware.”

Ya kara da cewa: Wannan batu bai shafi Gaza kadai ba, yana da alaka da zaman lafiya da aka dade ana nema a yankin gabas ta tsakiya.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted