Trump Ya Bada Umurnin Rage Tallafin Da Amurka Ke Ba Afrika Ta Kudu

Shugaban Amurka Donald Trump ya rattaba hannu a kan dokar da za ta rage tallafin da Amurka ke baiwa Afirka ta Kudu, wanda ake ganin

Shugaban Amurka Donald Trump ya rattaba hannu a kan dokar da za ta rage tallafin da Amurka ke baiwa Afirka ta Kudu, wanda ake ganin bai rasa nasaba da karar Isra’ila da Afrika ta Kudu ta shigar kan kisan gilla a Zirin Gaza da kuma kwace filaye

A ranar Juma’a ne fadar White House ta Amurka ta tabbatar da cewa Trump ya rattaba hannu kan wani kudiri na yanke tallafin kudi ga Afirka ta Kudu, saboda rashin amincewarsa da manufofinta na filaye, har ma da batun shigar da kara kan kisan gillar da ta yi a kotun kasa da kasa (ICJ) kan Isra’ila.

Gwamnatin Trump ta ba da misali da shari’ar da Afrika ta kudu ta jagoranta kan Isra’ila a kotun ICJ a watan Disamba na 2023, kan Washington da kawayenta.

Fadar White House ta kuma ce gwamnatin Trump za ta tsara wani shiri na sake tsugunar da manoman farar fata na Afirka ta Kudu da iyalansu. –

Trump dai bai bayar da wata shaida kan zargin da ya yi wa gwamnatin Afirka ta Kudu ba.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments