Togo: An Kashe Mutane 7 A Zanga-zangar Kin Jinin Gwamnati

Masu fafutuka a kasar Togo sun sanar da cewa an kashe mutane 7 a yayin Zanga-zangar nuna kin jinin gwamnati da aka yi a makon

Masu fafutuka a kasar Togo sun sanar da cewa an kashe mutane 7 a yayin Zanga-zangar nuna kin jinin gwamnati da aka yi a makon da ya shude, suna masu tuhumar  jami’an tsaro da yin amfani da karfin da ya wuce haddi.

Kamfanin dillancin labarun “Reuters” wanda ya nakalto ‘yan fafutukar na kasar Togo, suna cewa; Jami’an tsaro sun yi amfani da karfi mai ban tsoro akan masu Zanga-zangar.”

Kungiyoyin fararen hula da na masu kare hakkokin dan’adam  12 ne su ka fitar da sanarwar, su ka kuma kara da cewa; jami’an tsaron kasar sun yi amfani da kulake wajen dukan masu Zanga-zangar, haka nan kuma igiyoyi da suke daure su, kamar kuma yadda su ka sace da lalata dukiyar mutane.

Har ila yau kungiyoyin sun sanar da samun gawawwakin mutane 3 a ranar juma’ar da ta gabata, 2 daga cikinsu na kananan yara ne da aka jefa a cikin wani tafki a gabashin birnin Lome. Sai kuma gawawwaki 2 na wasu ‘yan’uwa a tafkin yankin Icodesio, shi ma a cikin birnin Lome. Sai a ranar Asabar ne aka sami cikon gawawwakin mutane 2  a yankin Niconakiboyi.

Bayanin da ya fito daga gwamnatin kasar a ranar Lahadi shi ne cewa, mutanen da aka samo gawawwakinsu sun nitse ne a cikin ruwa, tare da taya iyalan wadanda su ka rasa rayukan nasu alhinin rashin da su ka yi.

 Masu Zanga-zangar dai suna nuna kin amincewa da yin dandazon mukamkan gwamanti a hannun shugana kasar da kuma rashin Shata hanyar kawo karshen abinda suke ganin a matsayin kama-karya.

Kungiyar kare hakkin bil’adama ta “Amnesty International” ta bayyana abinda yake faruwa da ‘murkushe ‘yan hamayya.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted