Bola Ahmad Tinubu shugaban najeriya yayi alkawarin karbar bakuncin gasar wasannin kasasen renon ingila commom wealth a karon farko a shekara ta 2030 idan da rai da lafiya.
Shugaba tinubu ya bayyana hakan ne ta bakin shugaban hukumar wasanni ta kasa shehu dikko a lokacin da yake tarbar mambobin kungiyar ta common wealth a birnin tarayya Abuja a wani bangaren na kokarin da najeriya ke yi kan batun.
Malam Shehu Dikko ya bayyana cewa shugaban kasa bola Ahamd tunubu ya dauki alwashin dawo da wasanni a Afrika a karon farko,inda ya bayyana shi a matsayin wani babban matakin kara kusanto da mambobin kungiyar kusa,
A ci gaba da kokarin da gwamnati ke yi na ganin ta karbi bakunci shirya gasar, a shekara ta 2030 shugaban fadar shugaban kasa hon. Femi Gbajabiamila ya tarbi tawagar ta common wealth a madadin shgaban kasa Ahmad tunubu.