Fitaccen dan jarida na Amurka wanda Patrick Heili ya yi hira da shi ta Podcast, ya bayyana cewa; Shugaban kasar Amurka Donald Trump yana son ya ci gaba da zama akan kujerar mulki har abada.
Hirar da Thomas Friedman ta mayar da hankali ne akan salon mulkin Donald Trump da yadda yake son sauya yadda Amurka take a cikin kwanaki 100 na farkon mulkinsa.
Thomas Friedman ya ya bayyana yadda shugaba kasar ta Amurka Donald Trump yake kokarin kwaikwayon salon mulkin shugaban kasar China Xi Jin Ping da kuma na kasar Rasha Vladmir Putin da Fira ministan Isra’ila Benjamin Netanyahu.
Shi kuwa mai gabatar da shirin Patrick Heili ya yi ta’aliki da cewa, Trump yana kallon wadannan shugabannin a matsayin masu karfi a cikin duniyar da take cike da raunana, kuma shi Donald Trump yana son ya shimfida ikonsa a cikin duniya baki daya.