Telegraph: Birtaniya Ba Ta Da Karfin Da Za Ta Rika Kada Kugen Yaki

Jaridar Telegraph da ake bugawa a Birtaniya ta buga wata kasida da a ciki ta bayyana  zancen aikewa da sojojin kasar zuwa Ukiraniya a matsayin

Jaridar Telegraph da ake bugawa a Birtaniya ta buga wata kasida da a ciki ta bayyana  zancen aikewa da sojojin kasar zuwa Ukiraniya a matsayin abin dariya wanda yake son komawa da gaske bayan da ya kasance abin dariya.

Marubuciyar wannan kasida Allison Pearson ta ce ba a taba yin wani lokaci da fira ministan kasar ya zama abin dariya ba, kamar a kwanaki kadan da su ka gabata da ya mike a gaban majalisa ya yi barazanar aikewa da sojojin kasar zuwa Ukiraniya.

Haka nan kuma ta zargi Fira ministan kasar da cewa za su yi amfani da batun kara yawan taimakon soja ga Ukiraniya domin kara haraji a cikin gida.

Tun bayan da aka yi cacar baki a tsakanin shugabannin Amurka da na Ukiraniya ne dai, Donald Trump ya rattaba hannu akan dakatar da duk wani taimako na soja da kudade ga kieve, da hakan ya sa kasashen turai tunanin yadda za su cike gurbin Amurka.

Birtaniya da Faransa suna cikin na gaba-gaba wajen fito da tunanin yadda za su bai wa Ukiraniya taimakon da take da bukatuwa da shi,domin ci gaba da fada da Rasha.

Macron na Faransa ya bayyana cewa; Babu yadda za a yi turai ta bar Amurka ta zama ita ce mai ayyana makomarta, kuma zama ‘yan kallo akan abinda yake faruwa a duniya,yana da hatsari matuka.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments