Tel Aviv: Dubban yahudawa sun yi zanga-zangar adawa da yakin Gaza

Dubban mazauna birnin Tel Aviv ne suka taru a tsakiyar birnin a daren jiya Asabar, domin neman kawo karshen yakin Gaza, kwana guda bayan da

Dubban mazauna birnin Tel Aviv ne suka taru a tsakiyar birnin a daren jiya Asabar, domin neman kawo karshen yakin Gaza, kwana guda bayan da gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila ta sanar da shirin kara kai hare-hare da kuma mamaye birnin Gaza.

Masu zanga-zangar dai na dauke da allula da kuma hotunan wadanda ake tsare da su a Gaza, suna masu kira ga hukumomi da su ba da fifikon sakin su kan fadada ayyukan soji.

An kuma bayyana cewa hatta a cikin manyan jami’an soji na Isra’ila, babban hafsan hafsan hafsoshin sojin Isra’ila  Eyal Zamir ya yi yunkurin shawo kan majalisar ministoci kan cewa mamaye Gaza ba shi ne zabin da ya dace ba, da kuma tattauna babbar illar da hakan zai haifar ga tasirin soji da tattalin arziki a irin wannan hali, kamar dai yadda jaridar Isra’ila Hayom ta ruwaito.

Zamir ya kuma nuna damuwarsa kan yadda mamayar Gaza za ta shafi rayuwar fursunonin da ake tsare da su da kuma makomarsu.

Mai Magana da yawun sojin Isra’ila ya ce,  Zamir na bayar da shawarar a cimma matsaya, inda ya jaddada bukatar yin sassauci da kuma kara zage damtse wajen ganin an cimma yarjejeniya, ya kara da cewa rundunar sojin kasar ta nuna a shirye ta ke ta amince da duk wasu sharudda da suka hada da yarjejeniyar tsagaita bude wuta da za ta iya kawo karshen yakin.

A halin da ake ciki, ofishin Netanyahu ya sanar da cewa “Isra’ila” za ta karbe ikon birnin Gaza, ya kara da cewa “mafi rinjayen ministocin majalisar zartaswa sun yi imanin cewa shirin da aka gabatar wa majalisar ministocin ba zai cimma nasarar fatattakar Hamas ba ko kuma mayar da mutanen da aka yi garkuwa da su ba.”

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments