Tawagar wasannin Wushu na kasar Iran ta nuna rawar gani sosai a gasar hadin kan kasashen musulmi da ake yi a kasar saudiya inda ta samu lambobin yabo guda 4 wato Azurfa 1 tagulla 1 da kuma zinariya 2 a ranar karshe na gasa a wannan bangaren.
A bangaren mata kuma Sara shafi’I wacce ta fara fitowa a gasar kasa da kasa ta doke abokiyar hamayyarta daga kasashen kargyzstan da Turikiya ta kai ga wasan karshe , daga nan kuma ta yi galaba a kan abokiyar hammayarta ta kasar masar da ya kai ga bugun daga kai sai mai tsaron gida a zagayen farko don samu lambar zinariya
Haka zalika a bangaren mata masu nauyin kilograme 60 Sohaila Mansurian ta yi nasara akan abokiyar karawarta daga kasashen tunusiya da masar kuma ta samu lambar yabo ta zinariya ga kasar ta.
A bangaren masu nauyin kilo grame 70 kuma a gasar ta duniya Erfan muharrami bayan yayi galaba a akan abokin karawarsa daga masar Pakistan da kuma Afghanistan ya tunkari dan kasar kyrgirstan a wasan .