Tawagar kasar Iran ta maza da mata a wasan wushu a bangaren sanda da taolu ta samu gagarumar nasara inda ta samu lambobin yabo guda guda 10, zinariya 6 Azurfa guda 2 sai kuma tagulla guda 2, a wasan zakarun na washu karo na 17 da aka gudanar a kasar brazil,
Gasar Wushu ta duniya ita ce ta farko a gasar da kasar Sin ta mamaye. inda Iran ta samun kambun mataimakiyar zakara ta sha gaban manyan kasashe biyu kamar Malaysia da Hong Kong, ya nuna irin gagarumin sauyi a cikin tsarin wushu na duniya, kuma ya nuna irin kaifin basira da bangarorin biyu suke da shi na maza da mata.
Tawagar kasar Iran ta samu lambobin yabo guda 10 , ziniriya 6 Azurfa 2 sai kuma tagulla 2 a dukkan bangarorin sanda da kuma taolu, wannan yasa ta zo ta 2 a matsayin wadda ke bi ma wadanda suka zo na farko wato china, wannan shi ne karon farko cikin shekaru 6 da iran ta samu irin wannan gagarumar nasara