Ƙungiyar Raya Tattalin Arzikin Ƙasashen Yammacin Afirka (ECOWAS) za ta aika da wata babbar tawaga zuwa Bissau a wannan Litinin.
Tawagar, wacce shugaban ECOWAS na yanzu ke jagoranta, Shugaban Saliyo Julius Maada Bio, ta hada da shugabannin kasashen Senegal, Cape Verde, da Togo, ko wakilansu don ganawa da sabbin hukumomi, da manyan ‘yan siyasa da na farar hula, don tattauna sharuddan komawa ga tsarin mulki.
“Sakon zai kasance mai karfi,” in ji wata majiya kusa da tawagar ta ECOWAS.
Kafin nan sojojin da suka kwace mulki a Giunea Bissau sun sanar da cewa zasuyi mulkin rikon kwarya na shekara daya.
Tunda farko dama Kungiyar ta (ECOWAS) ta yi Allah wadai da juyin mulkin da ya faru a ranar Alhamis a kasar ta Guniea Bissau, kwanaki uku bayan zaben shugaban kasa da na ‘yan majalisu, inda ta kira shi da “barazana kai tsaye ga zaman lafiyar kasar da yankin.”
Wannan “juyin mulkin soja” ya zama “mummunan keta tsarin mulki” kuma “barazana kai tsaye ne ga zaman lafiyar kasar da yankin baki daya,” in ji ECOWAS a cikin wata sanarwa da ta fitar.
Ita ma Kungiyar Tarayyar Afirka, AU ta sanar da dakatar da kasar Guinea-Bissau daga zama mamba a kungiyar bayan hambarar da shugaban kasar, Umaro Sissico-Embalo da sojoji suka yi.