Mataimakin shugaban kasar Iran kan al-amuran na Musamman Muhammad Javad Zareef ya bayyana cewa tattaunawa kadai da Amurka, ba zai warware matsalolin Iran ba.
Kamfanin dillancin labarum IP na kasar Iran ya nakalto Zareef ya na fadar haka a taron majalisar ministocin da aka gudanar a jiya Laraba a nan Tehran.
Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iram ya kuma nakalto mataimakin shugaban kasar yana cewa, maslahar daga Amurka Itace ta dagewa takunkuman tattalin arziki. Wasu masana dadama, sun bayyana cewa idan trump ya na son tattaunawa da Iran to da dole ne ta farko Amurka ta dorawa iran sannan a yi maganar tattaunawa.
A jiya ne shugaban Trump ya bayyana anniyarsa ta shiga tattaunawa da kasar Iran yana kuma son haduwa da shugaban Ma’us Pajeskiyan. Amma duk tare da wadannan maganganu ba wanda yake Fatan shugaba Trump zai yi wani abu a kan hakan.