Hukumar Ƙididdiga a Najeriya, NBS ta ce arzikin cikin gida da kasar ke samu ya karu da kashi 4.23 cikin 100 a rubu’i na biyu na shekarar 2025 da muke ciki.
Sabbin alkaluman da hukumar ta fitar sun nuna cewa an samu karin kashi 3.48 idan aka kwatanta da irin wannan lokacin a 2024, lamarin da hukumar ta ce alamu ne na ingantar tattalin arzikin kasar.
Hukumar ta NBS ta ce fannin aikin gona ne kan gaba wajen samar da karuwar arzikin kasar, wannan ya karu zuwa kashi 2.82 sabanin kashi 2.60 a 2024.
Sauran fannonin da hukumar ta ce an samu ci gaba sun hada da fannin masana’antu da, da fan fetur da kuma fannin ma’adinai.
NBS ta ce a rubu’i na biyu na shekarar 2025, arzikin cikin gida da Najeriya ta samu ya kai naira tiriliyan 100.73, ƙari kan naira tiriliyan 84.48 da aka samu a 2024 daidai wannan lokacin, abin da ke nuna karin kashi 19.23 cikin 100.