Bayan hare haren da mutane suka kai kan ofisoshin jakadancin kasashen Ugandan, Rwandan, Kenyan, Japan, Amurka da kuma Faransa a birnin Kinshasa na kasar Democradiyya Congo masu zamga-zanga sun fara kwasar ganima a manya-manyan shaguwa a birnin.
Masu zanga-zangar sun fara tada hankali a kasar ne saboda irin saurin ci gaban da yan tawayen M23 suke mamayar kasar. Kuma suna ganin wadannan kasashe suna da hannu a tallafawa yan tawayen wadanda suke ci gaba da kwace garuruwa daga hannun sojojin Gwamnati.
Labarin ya kara da cewa an ga hayaki na tashi a ofishin jakadancin kasar Faransa a Kinshasa, kuma suna yin haka ne don nuna turjiya ga halayen mulkin mallaka na kasar faransa, wacce take daga cikin wadanda suke goyon bayan yan ta’addan.
A kwanakin da suka gabata dai kungiyar M23 dauke da makamai cikin kungiyoyi fiye da 100 dauke da makamai a arewacin yankin KIVU a DMC mai arzikin ma’adinan da ake bukatarsu a manya-manyan kamfanoni a duniya, ta kwace yankuna da dama daga ciki har da birnin goma babban birnin lardin.