Taron IMO : Tehran Ta Yi Watsi Da Zarge-zargen Isra’ila Marasa Tushe

Iran ta yi watsi da zarge-zargen da wakilan gwamnatin Isra’ila da gwamnatin Yemen mai murabus suka yi a zaman taron hukumar kula da harkokin teku

Iran ta yi watsi da zarge-zargen da wakilan gwamnatin Isra’ila da gwamnatin Yemen mai murabus suka yi a zaman taron hukumar kula da harkokin teku ta duniya (IMO) karo na 34.

A wata wasika da ta aike wa Sakatare Janar na IMO Arsenio Dominguez, Ofishin Jakadancin Jamhuriyar Musulunci ta Iran a kungiyar da ke Landan a ranar Laraba, ya bayyana damuwarsa game da yadd Isra’ila ke sarrafa hukumar IMO don manufofinta.

Wasikar ta jaddada cewa wannan dabi’a tana wargaza kwarewar hukumar ta Majalisar Dinkin Duniya a harkokin teku.

Tawagar Iran ta kara da cewa wadannan zarge-zargen marasa tushe wani bangare ne na wani tsari da Isra’ila ke kokarin lalata dokokin kasa da kasa, raunana hanyoyin da suka shafi bangarori daban-daban, da kuma kawo cikas ga ayyukan tsarin shugabanci na duniya.

A cikin wannan wasikar, Tehran ta bayyana wadannan zarge-zargen a matsayin “masu adawa” da “masu tayar da hankali,” tana ganin su a matsayin wani yunkuri na karkatar da hankalin kasashe mambobin IMO da keta dokokin kasa da kasa da Isra’ila ke yi akai-akai.

Wasikar ta kuma nanata ayyukan Isra’ila da suka sanya tsaron teku da ‘yancin zirga-zirgar jiragen ruwa cikin hadari, tana mai ambaton kame jiragen ruwan agaji na duniya da ke kan hanyarsu ta zuwa Gaza da sojojin Isra’ila ke yi yayin da jiragen ruwan ke yankin Falasdinawa.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted