Tare Da Taimakon Kasar China Za A Bude Masana’antun  Sarrafa Sanadarin Lithium A Nigerria

Kasar Najeriya ta sanar da Shirin fara aiki a wasu sabbin masana’antu domin sarrafa sanadarin Lithium Ministan ma’adanai na kasar ta Najeriya Daili Alaki ne

Kasar Najeriya ta sanar da Shirin fara aiki a wasu sabbin masana’antu domin sarrafa sanadarin Lithium

Ministan ma’adanai na kasar ta Najeriya Daili Alaki ne ya sanar a ranar Lahadin da ta wuce cewa, a wannan shekarar da ake ciki ta 2025, da hakan zai samar da gagarumin sauyi a fagen kayan da kasar za ta rika fitarwa zuwa kasashen waje.

Kamfanin dillancin “Reuters” ya ambato ministan ma’adanai na kasar yana ci gaba da cewa; ‘yan kasar China ne za su zuba hannun jari mafi grima a cikin wannan Shirin da hakan zai samar da ayyukan yi a cikin kasar da kuma bunkasar harkokin kere-kere.

Haka nan kuma Alaki ya yi ishara da cewa; Msana’antar sarrafa Lithium din da za a kafa akan iyakar jihohin Kaduna da Niger, za ta ci kudin da sun kai dalar Amurka miliyan 600, yayin da za a kafa wata matatar sanadarin na Lithium a  bayan birnin Abuja da kudin da sun kai dala miliyan 200.

Wata masana’antar ta sarrafa sanadarin Lithium da za kafa a tsakiyar wannan shekarar, za ta kasance ne a Jahar Nasarawa wacce ke iyaka da birnin Abuja.

  Majiyar ta kuma ambaci cewa kamfanin kasar China na ” Geoling’ da kuma “Kankakas Tecnalogy” ne su ka samar da kaso 80% na jarin  tafiyar da kamfanonin,yayin da za a samar da sauran kaso 20% daga cikin gida.

Tun a 2022 ne aka gudanar da wani bincike na karkashin kasa wanda ya tabbatar da cewa da akwai sanadarin “Lithium” a jahohi 6 na kasar, kuma yana da kyau sosai da kuma yawa,lamarin da ya ja hankalin kasashen duniya.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments