Tarayyar Turai Ta Yi Barazanar Karin Matsin Lamba Akan “Isra’ila”

Wasu jami’an diplomasiyyar turai sun yi wa gwamnatin Benjamin Netanyahu da cewa za ta fuskanci Karin matsin lamba idan har ba ta sauya halayyarta akan

Wasu jami’an diplomasiyyar turai sun yi wa gwamnatin Benjamin Netanyahu da cewa za ta fuskanci Karin matsin lamba idan har ba ta sauya halayyarta akan Gaza ba.

Jaridar “Washington Post” ta Amurka ta ambato jami’an diplomasiyyar turai suna cewa; sabon tsarin da ake yin aiki da shi na raba kayan agaji a Gaza, ya juya ya zama harigitsi kuma ana bude wuta akan mutane da hakan ya yi sanadiyyar jikkatar Falasdinawa da dama.”

Har ila yau jami’an diplomasiyyar na turai sun ce, ko kadan ba su da aniyar bayar da kayan agajinsu ga masu tafiyar da tsarin da su ne Isra’ila da Amurka.”

 Bugu da kari, majiyar diplomasiyyar ta tarayyar turai ta ci gaba da cewa; Hotunan masu ban tsoro da suke fitowa daga Gaza, sun kai musu iya wuya, ba za su iya ci gaba da jurewa ganinsu ba.”

A cikin kwanakin bayan nan dai kasashen turai sun fara yin matsin lamba akan HKI da ta bari a shigar da kayan agaji cikin yankin na Gaza da kuma yadda take ci gaba da kashe fararen hula da kuma rusau din da take yi mai yawa.

A karon farko, tun kirkirar HKI, kasar Jamus ta soki siyasar Tel Avi akan Gaza, da hakan yake nuni da yadda kasashen turai din suke kara matsin lamba.

Shugaban gwamnatin jamus  Friedrich Merz ya ce; Harin da Isra’ila ta kai wa wata makaranta a Gaza, ya tashi daga karkashin fada da ta’addanci, ya zama wani abu daban.”

A can kasar ta jamus din dai jam’iyyar hamayya ta ” Green Party” ta ce; bai kamata a rika amfani da makaman kasar Jamus a yakin Gaza ba.”

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted