Kungiyar tarayyar Afirka ta bayyana matukar damuwarta akan yadda al’amurra suke tabarbarewa a cikin kasar Mali, tana mai yin Ishara da yadda ‘yan ta’adda su ka killace iyakokin kasar da hana shigar da muhimman kayan bukatun rayuwa na yau da kullum.
Tarayyar Afirka ta kuma yi tir da yadda ake kashe farafen hula a kasar ta Mali da hakan yake haddasa rashin zaman lafiya da tsaro.
Bugu da kari, tarayyar Afirkan ta nuna cikakken goyon bayanta ga al’umma da kuma gwamnatin kasar Mali da iyalan wadanda aka kashe.
Kungiyar ta Afirka ta kuma nuna cewa a shirye ta bayar da dukkanin taimakon da ake bukatuwa da shi a kasar ta Mali domin samun zaman lafiya.
Kungiyar “Jama’atu Nusratul-Islam Wal Muslimin” mai alaka da alka’ida ce ta killace iyakokin kasar da ake shigar da kayan bukatuwar yau da kullum. A cikin watannin bayan nan an rika nuna fayafayen bidiyo na yadda ‘yan al’ka’idar suke kona jerin motocin jigilar makamashin da ake amfani da shi. A wasu yankunan kasar ma,kungiyar ta kone gidajen man fetur.
Kamfar makamashin da ake fama da ita a cikin kasar ya sam shugaban kasar Assimi Goita, ya yi kira ga al’ummar kasar da su rage yawan tafiye-tafiye akan Ababan hawa saboda a rage yawan bukatuwa da makamashin.