A Tanzaniyaan rantsar da Shugabar kasar Samia Suluhu Hassan a wa’adinta na biyu bayan ta lashe zaben da ya haifar da mummunar zanga-zanga a fadin kasar.
An ayyana Samia, wacce ta hau mulki a shekarar 2021 bayan mutuwar magabacinta, a matsayin wacce ta lashe zaben da aka gudanar a makon da ya gabata da kashi kusan 98.% na kuri’un da aka kada.
Tayi rantsuwar kama aikin ne a sansanin sojoji da ke Dodoma, babban birnin kasar.
Samia Hassan mai shekaru 65 ta fafata da ‘yan takara daga kananan jam’iyyu, yayin da manyan abokan hamayyarta daga manyan jam’iyyun adawa biyu aka haramta musu tsayawa takara.
Babbar jam’iyyar adawa a kasar ta ce an kashe daruruwan mutane a zanga-zangar.
Gwamnati ta yi watsi da mace-macen, tana mai cewa “an zuzuta alkalumman.”