Tanzania: An Tuhumi Mutane Da Dama Da Laifin Cin Amanar Kasa Bayan Rikicin Zabe

A yau Juma’a ne dai masu shigar da kara a Tanzania su ka gabatar da tuhumar mutane da dama da zargin cin amanar kasa, saboda

A yau Juma’a ne dai masu shigar da kara a Tanzania su ka gabatar da tuhumar mutane da dama da zargin cin amanar kasa, saboda rawar da su ka taka a cikin rikicin zaben shugaban kasa.

 Mutane 76 ne aka tuhuma da cewa; Sun yi kokarin kawo cikas akan zaben da aka yi a ranar 29 ga watan Oktoba da kuma tsokanar mahukunta a birnin Darussalam.

Baya ga laifin cin amanar kasa,ana kuma tuhumar mutanen da cewa sun kitsa aikata laifuka.

Zaben da aka yi a kasar Tanzani a karshen watan Oktoba, ya bar baya da kura saboda tashe-tashen hankulan da aka samu.

Babbar jam’iyyar adawa ta Chadema ta yi zargin cewa an kashe mutane fiye da 1,000,kuma a halin yanzu mahukuntan suna kokari boye duk wata shaida ta laifukan da su ka aikata ta hanyar binne gawawwaki a asirce.

Wadanda su ka sanya idanu a yadda aka gudanar da zaben sun ce, da akwai rashin gaskiya akan yadda aka gudanar da shi.

Shugabar kasar Samia Suluhu Hassan wacce ta hau karagar Mulki a 2021 bayan rasuwar magabacinta, ta lashe zaben da kawo 97% kamar yadda mahukuntan kasar su ka sanar.

Manyan ‘yan hamayya a zaben shugaban kasar da su ne Tundu Lissu daga jam’iyyar Chadema, da luhaga Mpina na jam’iyyar ACT-Wazalendo, an hana su shiga zaben da aka gudanar. Tarayyar Afirka ta ce masu sa ido da ta aike sun bayyana mata cewa;zaben bai hau ma’auninta na inganci ba.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments