Syria: Busaina Sha’aban Ta Karyata Labaran Da Aka Danganta Ma Ta Na Ganawa Da Jami’an Iraniyawa

Tsohuwar mai bai wa Basshar Asad na Syria shawara, Busaina Sha’aban ta kore gaskiyar labarin da aka rika watsawa na cewa ta yi wata ganawar

Tsohuwar mai bai wa Basshar Asad na Syria shawara, Busaina Sha’aban ta kore gaskiyar labarin da aka rika watsawa na cewa ta yi wata ganawar sirri da jami’an kasashen Iran, Iraki da Lebanon tare da Basshar Asad.

Busaina Sha’aban ta kuma ce ba ta yi managa da tsohon shugaban kasar ta Syria Basshar Asad ba akan labarun karya da aka watsa na cewa ya gana da jami’an dakarun kare juyin juya halin musulunci na Iran, ko kuma batun kafa sansanonin kungiyar al’ka’ida.

Ta kuma kara da cewa a tsawon rayuwarta ba ta taba ganawa da Shahid janar Kassim Sulaimani ba,ko shugaban rundunar “Hashdussha’abi” na janar Shahid Abu Mahdi al-muhandis.

Tsohuwar mai bai wa shugaban kasar ta Syria ta kuma ce; Labarun da aka watsa karya ce kirkirarriya wacce ba ta da tushe.

Busaina Sha’aban ta ce; Ban san dalilin da ya sa aka watsa wannan karyar a wannan lokacin ba, amma shi wanda ya yi hakan ya san manufarsa.

A wani labarin mai alaka daga Syria, shugaban kasar Ahmad al-Shara ya ce; Ko kadan kasarsa ba za ta yi wa “ Isra’ila” barazana ba.

Shugaban kasar ta Syria ya kuma ce; Tun daga lokacin da ya zama shugaban kasa, Syria ba ta tsokani Isra’ila ba.

Ahmad Shara ya kuma kara da cewa; Manufar kungiyarsu ta “Tahrir-Sham” shi ne kifar da gwamnatin Basshar Asad, kuma tun da hakan ta faru, ba  ta kai hari zuwa wata kasar waje ba.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments