Gwamnatin Sudan ta soki takunkuman da Amurka ta kakaba wa wasu daidaikun mutane da kamfanoni na kasar.
Cikin wata sanarwa da ma’aikatar harkokin wajen kasar ta fitar, ta ce irin wannan mataki da bangare guda ya dauka ba zai taimaka wajen cimma abubuwan da ake buri ba, ciki har da cimma zaman lafiya a Sudan, da kare tsaro da zaman lafiyar duniya.
Sanarwar ta ce, gwamnatin Sudan na bayyana cewa, hanya mafi dacewa ta warware rikici ita ce tattaunawa kai tsaye, maimakon dogaro da zato, wanda wasu masu manufa ta siyasa suka kitsa, wadanda ba su dace da muradun al’ummar Sudan ba.
Sanarwa ta nanata cewa, samun zaman lafiya a kasar, babban batu ne da al’ummarta a ko ina ke buri.
Ta kara da tabbatar da cewa, hakkin gwamnatin Sudan ne cika burin tabbatuwar zaman lafiya ta kowacce hanya, ciki har da tattaunawa da hada hannu da dukkan bangarori.