Jakadan Saudan a MDD Hassan Hamid ya bayyana cewa; Kasarsa tana yin kira ga kungiyoyin kasa da kasa da su kara matsin lamba akan UAE wacce take bai wa rundunar RSF makamai da sauran kayan soja.
Hamid wanda ya gabatar da taron manema labaru ya ce: ” Afili yake cewa daga ina ne rundunar RSF take samun makamai,abin takaici kuwa ba daga ko’ina ba ne sai HDL.
Jakadan na kasar Sudan a MDD ya yi kira da dakatar da bai wa wannan kungiyar ta ‘yan ta’adda makamai, ba tare da bata lokaci ba.
A can kasar Sudan ana ci gaba da fadace-fadace musamman a yankin Darfur.
Kungiyar kare hakkin bil’adama ta MDD ta fitar da bayanin dake cewa; ta sami rahotanni masu tayar da hankali, da su ka hada da yi wa mutane kisan gilla.
A baya sojojin kasar Sudan sun zargi rundunar kai daukin gaggawa ta RSF tana samun taimako daga HDL da makamai da kuma ‘yan ina da yaki daga kasashen Chadi, Libya, Kenya da Somaliya.
Daga cikin laifukan da ake zargin rundunar ta “Kai Daukin Gaggawa” da aikatawa da akwai cin zarfin mata da yi wa fararen hula kisan kiyashi sannan da wawason dukiyar mutane.
A ranar 26 ga watan Oktoba ne dai mayakan rundunar kai daukin gaggawar su ka kutsa cikin birnin Al-fasha, Babbar cibiyar yankin Darfur.