Bayanai daga Sudan ta kudu na nuni da cewa ana tsare damataimakin shugaban kasar na farko Riek Machar a wani gida, lamarin da MDD ta nuna matukar damuwa na yiwuwar komawar kasar wani yakin basasa.
Rahotanni sun ce a yammacin jiya Laraba jami’an tsaron Sudan ta Kudu sun tsare Riek Machar, kamar yadda kakakinsa ya sanar.
Ba a fayyace ainihin dalilin wannan tsarewar da kuma tasirinta ga dorewar yarjejeniyar zaman lafiya da aka rattabawa hannu a shekarar 2018 ba.
Tun a farkon watan Maris ne dai ake ta rade-radin kame Riek Machar, lokacin da rikicin yankin Upper Nile da ke arewa maso gabashin kasar ya kai ga kame wasu jami’an jam’iyyarsa a Juba.
tsare Mista Machar madugun ‘yan adawa na kasar na jefa shakku sosai kan shirin samar da zaman lafiya a Sudan ta Kudu a cewar masana.