Sudan: Mutane sama da rabin miliyan sun koma Khartoum duk da matsalar yaki

Hukumar kula da ‘yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya (IOM) ta bayar da rahoton a ranar Litinin cewa mutane sama da rabin miliyan ne

Hukumar kula da ‘yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya (IOM) ta bayar da rahoton a ranar Litinin cewa mutane sama da rabin miliyan ne suka koma Khartoum a cikin watan Yuli, wanda ke nuna karuwar komawa babban birnin Sudan da yaki ya daidaita.

A cewar hukumar, kimanin mutane 500,074 ne suka koma birnin, wanda ya karu da kashi 400 cikin 100 idan aka kwatanta da alkaluman da aka samu a watan Yuni.

Wannan ya biyo bayan kwato birnin ne da sojojin Sudan suka yi daga hannun mayakan Rapid Support Forces (RSF) a cikin watan Maris, a ci gaba da kokarin da gwamnatin kasar ke yi na kaddamar da shirye-shiryen sake gine-gine da kwantar da hankula.

Hukumar ta IOM ta lura cewa kimanin ‘yan Sudan miliyan biyu ne suka koma gidajensu a fadin kasar cikin watanni tara da suka gabata. An samu mafi yawan mutanen da suka dawo a jihar al-Jazira, sai kuma Khartoum, wadda yanzu haka ta karbi sama da mutane 600,000 da suka dawo baki daya.

Duk da wannan, Majalisar Dinkin Duniya ta yi gargadin cewa har yanzu ana cikin mawuyacin hali, tare da karancin samun damar gudanar da ayyukan yau da kullum da kuma barazanar sake barkewar rikici, musamman a yankunan da suka yi  fama da rikici.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted