Sudan : Janar al-Burhan Ya Shelanta ‘yantar Da Birnin Khartoum

Babban hafsan sojojin Sudan Janar Abdel Fattah al-Burhan, ya shelanta  ‘yantar da Khartoum Babban birnin kasar. Wannan na zuwa ne bayan da tun da farko

Babban hafsan sojojin Sudan Janar Abdel Fattah al-Burhan, ya shelanta  ‘yantar da Khartoum Babban birnin kasar.

Wannan na zuwa ne bayan da tun da farko ya sanar da cewa dakarunsa sun kwato filin jirgin saman babban birnin, wuri mai matukar mahimmanci daga hannun dakarun ‘yan tawaye na RSF.

“An ‘yantar da Khartoum, an gama,” in ji shugaban na Sudan daga fadar shugaban kasa a wani jawabi da aka watsa a gidan talabijin na kasar.

Kazalika, wata sanarwa da sashen watsa labarai na majalisar rikon kwarya mai mulkin kasar ta fitar, ta ce Al-Burhan ya sauka a filin jirgin sama na kasa da kasa dake birnin Khartoum ta jirgi mai saukar ungulu a jiyan, jirgin da ya zamo na farko da ya sauka a filin, tun bayan barkewar tashin hankali a watan Afrilun shekarar 2023.

Daga nan ne kuma ya duba sassan rundunar sojin gwamnati dake tsaron filin jirgin kafin ya wuce zuwa fadar gwamnati.

Tun daga farkon shekarar 2024, dakarun sojin gwamnati na SAF ke ta kwace sassan kasar daban daban, musamman a birnin Omdurman na arewacin Khartoum, inda suka kwace kaso mai yawa na birnin, lamarin da ya karfafa ikonsu sama da na dakarun RSF a yankin.

A ranar Juma’a data gabata, sojojin na sudan sun ayyana kwace iko da fadar gwamnati, da wasu muhimman ofisoshin gwamnatin kasar dake Khartoum, wuraren da a baya suka kasance muhimman sassa da dakarun RSF ke rike da su a birnin na Khartoum.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments