Firayi Ministan Spain Pedro Sanchez, ya yi kira ga sauran mambobin kungiyar Tarayyar Turai da su goyi bayan bukatar Madrid da Ireland na dakatar da yarjejeniyar ciniki bisa tsarin Free Trade da aka kulla tsakanin kungiyar EU da “Isra’ila” saboda ayyukanta na yaki a Gaza da Lebanon.
Spain da Ireland sun shafe watanni suna tattaunawa da sauran kasashen EU, suna neman yin nazari kan yarjejeniyar kungiyar EU da “Isra’ila”, tare da yin la’akari da keta yarjejeniyar hakkin dan Adam “Isra’ila” da Isra’ila take yi.
Firayi Ministan Spain Pedro Sanchez ya yi kira ga kasashen duniya kwanaki biyu da suka gabata da su dakatar da sayar da makamai ga “Isra’ila”, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na AFP ya ruwaito.
“Idan aka yi la’akari da abubuwan da ke faruwa a Gabas ta Tsakiya a halin yanzu, ya zama wajibi kasashen duniya su daina fitar da makamai ga gwamnatin Isra’ila,” in ji Sanchez bayan ganawa da Paparoma Francis a Roma.
Ya kuma bayyana rashin amincewarsa da ayyukan yakin Isra’ila, yana mai cewa, “Ina yin tir da Allah wadai da hare-haren da sojojin Isra’ila suka kai kan tawagar Majalisar Dinkin Duniya a Lebanon.”