Shugabannin kasashen Somaliya da Eritiriya sun tattauna kan karfafa huldar da ke tsakanin kasashen biyu da kuma wasu batutuwan da suka shafi shiyya-shiyya da na kasa da kasa, sannan kuma ministan harkokin wajen Somaliya ya musanta ba wa Habasha damar shiga tekun bahar maliya, yana mai bayyana wadannan kalamai a matsayin “zargi mara tushe.”
Shugaban kasar Eritiriya Isaias Afwerki da shugaban Somaliya Hassan Sheikh Mohamud sun tattauna kan karfafa alaka tsakanin kasashen biyu, baya ga batutuwan da suka shafi shiyya-shiyya da na kasa da kasa.
Afwerki ya jaddada bukatar ‘yantar da yankin daga shiga tsakani na kasashen waje, wanda galibi ke aiwatar da ajandarsu ta haifar da rikici da hargitsi a yankin.
Ya kara da cewa, “yarjejeniyar, wadda aka cimma a taron koli tsakanin shugabannin kasashen Eritrea, Somaliya da Masar, a birnin Asmara, ba ta da wasu manufofi illa karfafa dangantakar hadin gwiwa a tsakanin juna, da tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a Somaliya, da cin moriyar kasashen biyu.
A cikin wani yanayi mai alaka da hakan, ministan harkokin wajen Somaliya, Ahmed Moalim Faqi, ya yi tsokaci kan batun muradin gwamnatin Habasha na samun mashigar teku a Somaliya.
Ya ce babau wata Magana mai kama da hakan, a wani sakon da ya wallafa a shafinsa na dandalin “X” ya ce: “da’awar cewa an ba Habasha damar shiga tekun bahar maliyawadannan zarge-zarge ba su da tushe.”
Moalim Faqi ya jaddada cewa, Somaliya ta kuduri aniyar kare ‘yancin kanta da kuma harkokinta kasa.