Rundunar sojin Amurka ta kaddamar da wani hari ta sama a ranar Asabar din da ta gabata kan mayakan IS a yankin Puntland na Somalia, inda suka kashe wasu mambobin kungiyar da dama, a cewar rundunar sojin Amurka .
A cikin wata sanarwa da ta fitar, rundunar sojin Amurka da ke nahiyar Turai ta tabbatar da cewa, harin da aka kai tare da hadin gwiwar gwamnatin Somaliya, ya kashe da dama na mayakan ISIS a Somaliya.
Yayin da kungiyar IS ke hankoro hada karfinta a Somalia wanda bai bunkasa ba idan aka kwatanta da kungiyar Al-Shabaab mai alaka da Al-Qaeda, kungiyar ta mayar da hankalinta ne wajen kara fadada karfinta a yankin Puntland mai cin gashin kansa.
“Harin ya auke ne a kudu maso gabashin Bosasso, Puntland, a arewa maso gabashin Somalia,” in ji sanarwar.
Wannan farmakin ya biyo bayan wani harin makamancin haka ne kwanaki biyu da suka gabata, wanda AFRICOM ta bayyana a matsayin wani babban shiri na yaki da ta’addanci a Somaliya.
A cikin watan Fabrairu, hare-haren da Amurka ta kai kan kungiyar IS a Puntland, hukumomin yankin sun bayar da rahoton cewa an kashe “muhimman mutane”, ko da yake ba su bayar da karin bayani ba.
A wani mataki na kare martabar yankinta da kuma ja da baya kan rarrabuwar kawuna, rahotanni sun ce Somaliya ta bai wa Amurka damar iko kan muhimman tashoshin jiragen ruwa da sansanonin jiragen sama dake Somaliland da Puntland.