Sojojin Yemen Sun Sake Kai Wa HKI Hari Da Makami Mai Linzami

Sojojin kasar Yemen sun sake kai wani hari da makali mai linzami da safiyar yau Talata wanda ya sa jiniyar gargadi ta kada a cikin

Sojojin kasar Yemen sun sake kai wani hari da makali mai linzami da safiyar yau Talata wanda ya sa jiniyar gargadi ta kada a cikin yankuna da dama na HKI.

Wannan dai shi ne karo na 3 a cikin sa’o’i 24 da kungiyar Ansarullah ta Yemen ya harba wa HKI makamai masu linzami.

Sojojin HKI sun bayyana cewa, makamin da aka harbo daga Yemen ya sa jiniyar gargadi ta kada a cikin yankuna masu yawa a Falasdinu dake karkashin mamaya.

Yemen dai tana kai wa HKI hare-hare ne saboda taimaka Falasdinawa dake yi wa kisan kiyashi fiye da shekara daya da rabi,wanda kuma har yanzu bai tsaya ba.

Shugaban kungiyar Ansarullah Sayyid Abdulmalik Husi ce; matukar ba a kawo karshen yakin Yemen ba, to ba za su daina kai wa manufofin HKI hare-hare ba.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments