Sojojin Yemen Sun Kai Zafafan Hare-Hare Kan Haramtacciyar Kasar Isra’ila Guda Uku  

Sojojin Yemen sun sanar da kai wasu zafafan hare-hare guda 3 kan mayakan sojojin yahudawan sahayoniyya ‘yan mamaya Rundunar Sojin kasar Yemen ta sanar da

Sojojin Yemen sun sanar da kai wasu zafafan hare-hare guda 3 kan mayakan sojojin yahudawan sahayoniyya ‘yan mamaya

Rundunar Sojin kasar Yemen ta sanar da cewa: Sojojinta sun kai wasu jerin zafafan hare-hare guda uku da jiragen saman yakin soji marasa matauka ciki, inda hare-haren suka janyo barna a muhimman wurare uku na makiya sojojin mamayar Isra’ila.

A cikin wata sanarwa da rundunar sojin kasar ta Yemen ta fitar ta bayyana cewa: Wadannan hare-hare wani bangare ne na matakin da ya dace na mayar da martani ga hare-haren wuce gona da iri da sojojin mamayar Isra’ila ke kai wa kan zirin Gaza.

Sannan sanarwar ta kara da cewa: Farmakin na farko an kai shi ne yankin Jaffa da aka mamaye da jirage marasa matuka ciki guda biyu. Harin na biyu ya biyo an kai shi ne kan yankin Ashkelon. Sannan harin na uku an kai ne kan wani gungun sojojin mamaya a yankin Negev.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted