Sojojin Yemen sun kai wani gagarumin hari kan wani jirgin ruwa a tekun Bahar Maliya da ke da alaka da yahudawan sahayoniyya
Rundunar sojin Yemen ta sanar da cewa: Sojojinta sun kai farmaki kan jirgin (Anadolu S) a cikin tekun Bahar Maliya da wasu makamai masu linzami na ballistic da suka dace, kuma harin ya samu daidai yadda aka saita shi.
Rundunar sojin kasar ta Yemen bayyana a cikin wata sanarwa da ta fitar cewa: Sojojinta sun kaddamjar da wannan hari ne kan jirgin ruwan saboda bai mutunta gargadin da sojojin Ruwan Yemen suka yi masa ba, sannan kuma kamfanin da ya mallaki jirgin ruwan ya keta dokar hana shiga tasoshin ruwa na Falasdinu da aka mamaye.
Sojojin na Yemen sun jaddada aniyarsu ta ci gaba da kakaba takunkumi kan makiya yahudawan sahayoniyya a teku ta hanyar hana duk wani jirgin ruwa da ke da alaka da haramtacciyar kasar Isra’ila wucewa ta tekun Bahar Maliya, kuma wannan takunkumi ba zai tsaya ba, har sai yahudawan sahayoniyya sun kawo karshen kai hare-haren wuce gona da iri kan Gaza da Lebanon.