Sojojin Yemen sun kai hari kan filin jirgin saman Ben Gurium a wani aiki na musamman na tallafawa al’ummar Gaza
Sojojin Yemen sun sanar da kai wani gagaruminj hari kan tashar jirgin saman Lod da ke yankin Jaffa da aka mamaye ta hanyar amfani da makami mai linzami kirar Falasdinu 2.
Hari ya gudana daidai inda aka tsara shi, kuma ya haifar da firgici da ya kai ga miliyoyin yahudawan sahayoniyya gudu tare da shigewa maboyar karkashin kasa kamar burage. Har ila yau, harin ya dakatar da dukkan ayyukan filin jirgin, tare da hana wani jirgin dakon kaya na sojan Amurka sauka a filin jirgin sama na Ben Gurium a rana ta biyu a jere.
A cikin wannan yanayi ne rundunar sojin Yemen ta jadadad cewa: Makiya yahudawan sahayoniyya masu laifi, ba za su taba samun sassauci ko rangwame daga sojojin Yemen ba, sai karin fuskantar hare-hare da makamai masu linzami da jiragen sama marasa matuka ciki, don mayar da martani kan laifukan da suke aikatawa kan al’ummar Falastinu.