Sojojin Yemen Sun Harbo Jirgin Leken Asirin Amurka Samfurin MQ9

Kakakin sojojin Yemen Janar Yaha Sari ya sanar da cewa, sun harbo jirgin leken asirin Amurka samfurin MQ9 a saman yankin Ma’arib. Janar Sari ya

Kakakin sojojin Yemen Janar Yaha Sari ya sanar da cewa, sun harbo jirgin leken asirin Amurka samfurin MQ9 a saman yankin Ma’arib.

Janar Sari ya ci gaba da cewa za mu ci gaba da abinda muke yi na hana jiragen ruwa wuce ta tekun “Red Sea” domin zuwa HKI, tare da kara da cewa, ba kuma za mu yi taraddudin daukar dukkanin matakan kare kai ba, akan jiragen ruwan abokan gaba a nan gaba.

Kwanaki biyu da su ka gabata, sojojin Yemen sun kai wasu hare-hare akan jirgin dakon jiragen yaki na “Trauman’ da sauran jiragen yakin da suke ba shi kariya.

Sojojin na Yemen suna kuma ci gaba da kai wa HKI hare-hare da jiragen sama marasa matuki da kuma makamai masu linzami a karkashin taya Falasdinawa fada, da kuma yin kira da a kawo karshen takunkumin da aka kakaba musu.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments