Sojojin Yamen Sun Cilla Wani Makamai Masu Linzami Kan HKI

05-Majiyar Sojojin kasar Yemen ta bayyana cewa sojojin kasar a safiyar yau ma sun cilla makamai masu linzami a kan tashar jiragen sama na Bengerion

05-Majiyar Sojojin kasar Yemen ta bayyana cewa sojojin kasar a safiyar yau ma sun cilla makamai masu linzami a kan tashar jiragen sama na Bengerion a birnin Yafa (telaviv) na HKI. Inda faduwar makaman ya dakatar da sauka da tashin jiragen sama a tashar. 

Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto Janar Yahyah Sari yana fadar haka a yau, ya kuma tabbatar da cewa, makamin samfurin Bilistic ya sami bararsa kamar yadda aka tsara.

Ya ce faduwar makamin ya dakatar da dukkan ayyukan sauka da tashin jiragen sama a wannan tashar banda haka cilla makamai ya sa miliyoyin yahudawa rugawa zuwa wararen buya.

Tun watan maris da ya gabata ne sojojin yahudawan sahyoniyya suka sake farfado da yaki a kan Falasdinawa a Gaza, kuma suka hana shigar abinci zuwa yankin, wanda ya sa gwamnatin kasar Yemen, banda hana jiragen kasuwancin yahudawan wucewa ta Red sea ta kuma fara cilla makamai kan tashar jiragen sama mafi girma a HKI har zuwa lokacinda ta daina yaki a gaza ta kuma bude kofofin shiga yankin don isar kayakin abinci.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments