Rahotanni sun bayyana cewa wasu masu dauke da makamai sun kama shugaban kasar Guinea Bissau Umaro Sissoco Embalo a yau Laraba, kwanaki uku bayan da aka yi zaben shugaban kasa.
Rahotannin sun ce an yi ta harbe harbe a babban birnin kasar, a yayin da Alummar kasar ke zaman jiran sakamako zagaye na farko na zaben shugaban kasa da aka yi a ranar Lahadi.
Zuwa yanzu ba a tabbatar da ko su wane ne suka yi harbin ba.
Rahotannin sun kuma ce an yi ta harbe harben a kusa da fadar shugaban kasar da ofishin hukumar zabe a yau Laraba, inda mutane suka tarwatse suna neman mafaka.
A jiya Talata ne dai shugaban mai ci Umaro Sissoco Embalo, da babban abokin hamayyarsa Fernando Dias, suka yi ta ikirarin yin nasara a zaben wanda ya kamata a yi tun a shekarar da ta gabata.
Guinea Bissau dai ta fuskanci juyin mulki har karo hudu da rashin zaman lafiya tun bayan samun ƴancin kai daga Portugal a 1974.