Majiyoyin sojin Sudan sun sanar da cewa: Sun sake samun nasarar kwace iko da babban birnin kasar Khartoum
Majiyoyin sojin Sundan sun sanar da cewa: Cikin dan gajeren lokaci sun samu nasarar sake kwace iko da birnin Khartoum fadar mulkin kasar daga mamayar dakarun kai daukin gaggawa na Rapid Support Forces, bayan da suka yi birnin kawanya daga bangarori hudu.
A nata bangaren, Ma’aikatar yada labaran Sudan ta zargi bangarorin waje da jagorantar gudanar da fadace-fadacen da ‘yan tawayen dakarun kai daukin gaggawa ke yi don samun damar cin gajiyar albarkatun kasar, idan ‘yan tawaye suka yi nasara.
Rayuwa ta fara inganta a birnin Omdurman kuma kasuwanni sun fara farfadowa, inda jama’a suke komawa ci gaba da harkokinsu na yau da kullum ciki har da garuruwan Kassala da Port Sudan tare da tafiye-tafiye zuwa birnin Khartoum fadar mulkin kasar, tare da cewa an fara aikin sake gina kasar ayankunan da aka samu kwanciyar hankali, amma har yanzu ana cikin damuwa da fargaba a birnin Khartoum sakamakon hare-haren bama-bamai da dakarun kai daukin gaggawa ke kai wa ta sama musamman kan asibitoci da kasuwanni.