Bayan kwace iko da cibiyar gundumar Jazira, ta Wad Madani a jiya Asabar, sojojin suna kokarin kwace iko da babban birnin kasar Khartum da rundunar kai daukin gaggawa take rike da wasu sassa nashi.
Sojojin na Sudan sun kai hare-hare akan Khartum Bahri da kuma Khartum da manyan bindigogi da zummar korar rundunar kai daukin gaggawa daga ciki.
Bugu da kari, sojojin na Sudan sun sanar da kwace iko da yankin duwatsun –al-bakkash’ dake zagaye da kamfanin tace man fetur din kasar, bayan da aka yi fada mai tsanani.
Rundunar Sojan kasar ta Sudan ta yi alakwalin kwace iko da dukkanin yankunan da suke a karkashin ikon rundunar daukin gaggawa da Hamidati Duklu yake jagorancta.
A jiya Asabr mutanen garuruwan Um-Durman da Port Sudan sun yi bukukuwa na murna saboda kwato garin Wad-Madni da sojoji su ka yi.