Sojojin Sudan Suna Ci Gaba Da Samun Nasara A Akan Dakarun Kai Daukin Gaggawa

A yau Alhamis sojojin na kasar Sudan sun sanar da abinda su ka kira; Yin shara a cikin birnin Khartum, domin gano inda gyauron mayakan

A yau Alhamis sojojin na kasar Sudan sun sanar da abinda su ka kira; Yin shara a cikin birnin Khartum, domin gano inda gyauron mayakan dakarun rundunar sa-kai suka buya.

Haka nan kuma sojojin na Sudan sun sanar da sakin farsunoni masu yawa da rundunar kai daukin gaggawa din suka tsare su, a lokacin da suke rike da birnin na Khartum.

Sojojin kasar ta Sudan sun nuna shugaban majalisar sojan kasar Janar Burhan  a cikin fadar shugaban kasa, inda ya sanar da cewa; An ‘yanto da Khartum.

A karon farko jirgin  Janar Burhan ya sauka a filin saukar jiragen sama na Khatrum, tun bayan da yaki ya barke.

Tun a jiya Laraba ne dai  sojojin na Sudan su ka sanar  da shimfida ikonta akan filin saukar jiragen sama na Khartum wanda shi ne tunga ta karshe da ta saura a hannun rundunar kai daukin gaggawa.

Kwamandan rundunar sojan Sudan da take fada a birnin na Khartum Lafatnar kasar Abdurrahman al-Bilawi ne ya sanar da cewa, an  shimfida iko a  cikn filin saukar jiragen sama na kasa da kasa na birnin Khartum.

Har ila yau kwamandan sojan ya kuma bayyana cewa, a yanzu haka suna cigaba da faraurar mayakin “Rundunar Kai Daukin Gaggawa”da su ka saura a cikin binin Khartum.

Kwanaki kadan da su ka gabata ne dai sojojin na Sudan su ka kwato fadar shugaban kasa wacce ta dauki shekaru biyu a hannun rundunar kai daukin gaggawa, haka nan kuma babbar cibiyar soja da tsakiyar birnin Khartum da can ne ma’aikatu da dama suke.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments