Sojojin Sudan Sun Tsananta Kai Hare-Hare Kan ‘Ya Tawayen Rapid Support Forces

Sojojin Sudan na ci gaba da gudanar da ayyukansu na kai farmakin karshe da nufin murkushe ‘yan tawayen Dakarun Kai Daukin Gaggawa Sojojin Sudan sun

Sojojin Sudan na ci gaba da gudanar da ayyukansu na kai farmakin karshe da nufin murkushe ‘yan tawayen Dakarun Kai Daukin Gaggawa

Sojojin Sudan sun fara aikin wanzar da tsaro a wasu yankuna a jihar Al-jazira da ke tsakiyar kasar Sudan, tare da kara tsaurara matakan killace fadar shugaban kasar da ke karkashin ikon dakarun kungiyar Rapid Support Forces, wadanda a halin yanzu mayakan ‘yan tawayen suke fama da karancin kayayyakin aiki.

Sojojin Sudan sun kai farmaki kan dakarun kai daukin gaggawa na Rapid Support Forces da ke kusa da gadar Soba, wadda ta hada kudancin Khartoum da gabashin Nilu a kan hanyar kogin Blue Nile, inda suka kwace iko da sansanonin dakarun ‘yan tawayen. A yayin da Dakarun kai daukin gaggawa suka yi ruwan bama-bamai a yankuna da dama na Gabashin Nile da Umm Dom a birnin Khartoum, inda suka kashe fararen hula 7 tare da jikkata wasu da dama.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments