Sojojin Sudan Sun Kwace Iko Da Birnin Umm Rawaba A Jihar Kordofan Ta Arewa

Sojojin Sudan sun kwace iko da wani birni da ke arewacin Kordofan daga hannun ‘yan tawayen kasar na Rapid Support Forces Rundunar sojin Sudan ta

Sojojin Sudan sun kwace iko da wani birni da ke arewacin Kordofan daga hannun ‘yan tawayen kasar na Rapid Support Forces

Rundunar sojin Sudan ta sanar da cewa ta sake kwace iko da birnin Umm Rawaba, birni na biyu mafi girma a arewacin jihar Kordofan da ke kudancin kasar daga hannun dakarun kai daukin gaggawa na Rapid Support Forces.

A cikin wata sanarwa da rundunar sojin Sudan ta fitar ta ce: Godiya ta tabbata ga Allah da yardarSa, sojojin sun tsarkake birnin Umm Rawaba daga hannun mayakan dakarun kai dauki gaggawa da sojojin hayarsu, tare da janyo musumunanan hasarori masu yawa.

A cewar shafin yanar gizo na Arabi 21, Dakarun kai daukin gaggawa na Rapid Support Forces sun mamaye birnin Umm Rawaba ne tun daga watan Satumban shekara ta 2023, wanda ke da tazarar kilomita 145 daga birnin Al-Abyadh, babban birnin jihar Kordofan ta Arewa.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments