Sojojin Sudan Da ‘Yan Tawayen Kasar Suna Ta Musayar Kai Hare-Hare Kan Junansu

Jiragen yaki marasa matuka ciki sun kai hare-hare kan sansanin sojin ruwa mafi girma a Port Sudan Sojojin tsaron saman Sudan sun dakile wani harin

Jiragen yaki marasa matuka ciki sun kai hare-hare kan sansanin sojin ruwa mafi girma a Port Sudan

Sojojin tsaron saman Sudan sun dakile wani harin da jirgin sama maras matuki ciki ya yi niyyar kai wa kan mafi girman sansanin sojin ruwan kasar da sanyin safiyar Laraba, in ji wata majiyar soji. Wannan dai shi ne rana ta hudu a jere da ake kai hare-hare kan birnin Port Sudan da ke karkashin ikon gwamnati.

Majiyar wadda ta bukaci a sakaye sunanta ta ce, jiragen saman yakin marasa matuka ciki sun kai hari kan sansanin sojin ruwa na Flamingo, kuma na’urorin kakkabo makamai masu linzami suna kakkabo makaman da aka harba. Tsawon rabin sa’a ana jin karar makaman roka masu linzami da aka yi amfani da su a kasa da kuma wasu bama-bamai da suka samo asali daga arewacin Port Sudan, inda sansanin sojin ruwa yake.

Port Sudan dai ita ce wurin zama na wucin gadi na gwamnatin kasar, lamarin da ya sanya ta zama hedkwatar rikon kwarya bayan barkewar yaki tsakanin sojojin Sudan da dakarun kai daukin gaggawa na Rapid Support Forces.

Tun a watan Afrilun shekara ta 2023 ne Sudan ta fada cikin kazamin rikici tsakanin kwamandan sojojin kasar Janar Abdel Fattah al-Burhan, wanda shi ne shugaban Majalisar Gudanar da Mulkin kasar tun bayan juyin mulkin shekarar 2021, da kuma tsohon mataimakinsa, Janar Mohamed Hamdan Dagalo, kwamandan dakarun kai daukin gaggawa na Rapid Support Forces.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments