Sojojin mamayar Isra’ila suna ci gaba da kai farmaki kan birnin Tulkarm da sansaninsa da ke gabar yammacin kogin Jordan
Sojojin mamayar gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila sun shiga rana ta shida suna kai hare-haren wuce gona da iri kan birnin Tulkarm da sansaninsa, inda yanayin tsoro da tarwatsa gine-gine suka lullube mazaunan yankunan, adaidai lokacin da sojojin mamayar Isra’ila suke ci gaba da kai hare-hare da kutsawa cikin gidajen Falasdinawa, lamarin da ya yi sanadin barnatar da dukiyoyin Falasdinawa da dama tare da tilastawa iyalai masu yawa tsarewa zuwa gudun hijira.
Sojojin mamayar Isra’ila suna gudanarda sintiri da kafa ta hanyar gudanar gudanar da yawo a kan tituna a cikin birnin musamman a yankunan yamma, kudanci da kuma gabas, inda suka kai farmaki gidajen Falasdinawa tare da bincikar gidajen da kuma kaihare-hare kan barikokin soji gami da tura ‘yan sari ka noke a kan rufin gidaje.