Sojojin haramtacciyar kasar Isra’ila sun kai wasu mummunan hare-hare kan yankunan tsakiya da kuma yammacin kasar Siriya
Majiyar watsa labaran Siriya ta bayar da rahoton cewa: Da sanyin safiyar yau litinin, sojojin yahudawan sahayoniyya sun kai wasu jerin munanan hare-hare kan yankunan biranen Hama da Homs da suke tsakiyar kasar Siriya da kuma Tartous da Latakia a yammacin kasar, hare-haren an kai sune da jiragen saman yakin yahudawan sahayoniyya kan sansanonin sojin Siriya da suke wadannan yankuna.
Majiyar ta kara da cewa: Hare-haren wuce gona da irin spjpjin haramtacciyar kasar Isra’ila kan kasar Siriya sun fi mai da hankali ne kan sansanonin sojin kasar da wuraren da suke dauke da na’urorin kariya, musamman kan sansanonin makamai masu linzami ciki har da barikin 107 da ke yankin Zama da ma’ajiyar makamai a cikin karkarar Tartous, ba tare da samun wani bayani kan hasarar mutane ba.