Kusan sojoji 1,300 ne kungiyar kasashen gabashin Afirka ta SADC su ka fice daga kasar jamhuriyar Demokradiyyar Congo, a lokacin da mayakan kungiyar ‘yan atwaye ta M23 suke cigaba da kama yankunan kasar.
Wani mai sharhi akan al’amurran siyasar kasar ta Congo, Christian Moleka ya yi gargadi akan sake dagulewar al’amurra a gabashin kasar wanda dama can yana fama da matsalolin tsaro.
Janyewar da sojojin na SADC su ka yi daga cikin kasar tana a matsayin wani babban koma baya ne, alhali gwmanatin Kinshasha tana fatan ganin wadannan sojojin sun taka rawa wajen takawa mayakan M23 birki,kamar yadda su ka taba yi a 2023.
Sojojin na Congo suna fama da karancin kayan aiki da makamai, da hakan ya bai wa mayakan M 23 damar kwace iko da Goma da Bukavu.
Ana zargin kasar Rwanda da cewa ita ce ke taimaka wa ‘yan tawayen na M23, tare da aike sojoji 4000 da suke yaki a tare da ita.
A gefe daya, hukumar Agaji ta MDD tana yin kira ga kungiyoyi kasa da kasa da su taimaka su hana bullar babbar matsalar ‘yan gudun hijira da tabarbarewar harkokin agaji a cikin kasar.