Sojojin Kasar Siriya Sun Tilastwa Yan Ta’adda A Yankunan Halab Da Idlib Na Kasar Siriya Jada Baya

Majiyar sojojin gwamnatin kasar Siriya ta bada sanarwan cewa, sun sami nasara a kan yan ta’adda masu samun goyon bayan kasashen yamma, inda suka tilasta

Majiyar sojojin gwamnatin kasar Siriya ta bada sanarwan cewa, sun sami nasara a kan yan ta’adda masu samun goyon bayan kasashen yamma, inda suka tilasta masu jada baya a lardunan Halab da kuma Idlib wadanda suke hannun sojojin gwamnati cikin yan kwanaki biyu da suka gabata.

Kamfanin dillancin laraban IP na kasar Iran ya nakalto ma’aikatar tsaron kasar Siriya na bada sanarwan tilastawa mayakan yan ta’adda ta ‘Hai’atu Tahriri Shama” da wasu kungiyoyin, jada baya daga yankunan da suka mamaye a lardunan Halab da kuma Idlib a ranakun Laraba da Alhamis da suka gabata.

Majiyar ta kara da cewa sojojin Siriya tare da taimakon jiragen yaki na kasar Rasha sun tilastawa yan ta’addan janyewa daga wuraren da suka mamaye a ranakunan Laraba da kuma Alhamsi da suka gabata.

Tashar talabijin ta Almayadeen ta kasar Lebanon ta bada labarin cewa an kashe yan ta’adda kimani 400 a fafatawar kwanaki biyu da suka gabata. Kuma sun dawo da ikon gwamnatin kasar Siriya kan garuruwan Al-Baqoum, Bashantra da Bashqatin a cikin lardunan guda biyu a safiyar yau Jumma’a.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments