Ma’aikatar tsaron kasar Rasha ta sanar da mutuwar ‘yan ta’adda da dama dauke da makamai a harin da sojojin Siriya tare da hadin gwiwa da sojojin Rasha suka kai kan maboyarsu a arewacin Latakiya. A cewar sanarwar da rundunar sojin Rasha ta fitar, an kuma kama wasu jiragen sama marasa matuka da ‘yan ta’adda suka aika zuwa kudancin Idlib.
A nata bangaren ma’aikatar tsaron kasar ta Siriya a wata sanarwa da ta fitar a shafinta na Facebook ta bayyana cewa: Rukunonin dakaru na sojojin Siriya da ke kan hanyar zuwa arewacin Latakiya tare da hadin gwiwar mayakan kasar Rasha sun kai hari kan maboyar ‘yan ta’adda, lamarin da ya kai ga ragargaza wurin gaba daya, tare da kashe da kuma raunata da dama daga cikinsu, ciki har da shugabannin kungiyar ta’addancin da ake kira “Hizb Turkistani “.
An bayyana a cikin wannan sanarwa cewa: Rukunonin da ke aiki a kan hanyar zuwa yankunan kudancin kasar Siriya a lokacin da suke mayar da martani kan harin da kungiyoyin ‘yan ta’adda masu dauke da makamai suka yi, sun yi barna mai yawa a kan kayayyakin ‘yan ta’addan da makamansu, lamarin da ya yi sanadin mutuwa da jikkatar daga cikin ‘yan ta’adda.
Sanarwar ta kara da cewa: Sojojin Siriya sun kuma yi nasarar lalata wasu jirage marasa matuka masu kunar bakin wake da ‘yan ta’adda da ke shirin kai hari da su kan wuraren soji da kauyuka da garuruwa masu aminci a kasar ta Siriya.