Sojojin Kasar Faransa Sun Fara Ficewa Daga Kasar Chadi

Ma’aikatar tsaron kasar Chadi ta bada labarin cewa kasar Faransa ta fara janye sojojinta daga kasar Chadi a jiya Jumma’a. Bayan da wa’adin zamansu a

Ma’aikatar tsaron kasar Chadi ta bada labarin cewa kasar Faransa ta fara janye sojojinta daga kasar Chadi a jiya Jumma’a. Bayan da wa’adin zamansu a kasar ta chadi ya ciki, kuma gwamnatin kasar ta ki sabonta yarjeniyar kamar yadda ta saba a baya.

Tashar talabijin ta Presstv a nan taehran ta bayyana cewa, labaran da suke fitowa daga kasar ta Chadi sun nuna cewa an ga sojojin kasar ta Faransa suna shiga jirgin saman yaki na kasar Faransa a birnin Njamaina a kokarin  ficewa daga kasar.

Kasar faransa dai tana da sojoji kimani 1000 guda a cikin kasar ta Chadi, sannan ana saran ficewarsu gaba daya zai dauki watanni kafin hakan ya tabbata.

Kasar Faransa dai ta kawo sojojinta a kasar Cahdi tun bayan samun yencin kan kasar a shekara 1960. Har yanzun dai ba’a sani ba ko wasu yan kadan daga ciki sojojin zasu ci gaba da zama a kasar bayan ficewar mafi yawansu.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments